24/08/2026
https://www.facebook.com/61580917514421/posts/122136700947030583/
Wani matashi kuma Na Gaba Gaba a harkar siyasar Jamiyyar APM a jihar Bauchi Alhaji kamilu mu,azu Abubakar [shatiman Boto] ya Bayyana cewa Tabbas Alummar jihar Bauchi Ba zasuyi Nadama Ba wajen Zaben Maigirma Gwamnan jihar Bauchi sanata Bala Abdulkadir Muhammed kauran Bauchi a Matsayin sanatan Bauchi ta kudu a Zabe mai zuwa Na 2027 Da kuma Tsohon kwamishinan kudi Wato Hon yakubu Adamu PhD.
Yace Duba da yadda Gwamna Bala ya tafka ayyuka na Mahdi ka ture a jihar Bauchi da kewaye Wanda kowa ya shaida Hakan Ba Abu Ne Boyayye Ba ya cancanta a zuba masa Ruwan kuri,u ne Ranar Zabe Domin samun damar cigaba da Ayyukan Alkhairi ga Alummah.
A Daya Bangaren kuwa
Alhaji kamilu mu,azu yace Bada Dama wa Hon Yakubu Adamu PhD yazama gwamna a jihar Bauchi zai sake bude Wani sabon shafi Na cigaba daga inda Mai Girma Gwamna ya tsaya.
Yakuma Nemi Goyon Bayan matasa A Ko ina daga jihar Bauchi da su shigo Wannan tafiyar Nasara ta jamiyyar APM Don kafa tubalin Alheri.
lokaciyayi24/7